‘Dan Boko Haram din da aka kama ya sami tsallake shingayen jami’an tsaro da dama har zuwa wani rukunin gidajen gwamnati dake kusa da fadar jihar, kafin dubun sa ta cika.
Kwamandan tsaron rundunar ta Civil defense a jihar Adamawa, Aliyu Musa Ndanusa, ya gurfanar da wanda aka kaman ga manema labarai a Yola, inda yace mututmin mai suna Amos Hassan, dan shekara 25 a duniya an kama shi ne a Federal Housing Estate dake kusa da fadar jihar bayan ya gudo daga dajin Sambisa.
Suleiman Baba dake zama jami’in hulda da jama’a na rundunar civil Defense a jihar Adamawa yace sun sha kama yan Boko Haram.
A kowanne lokaci hukumomin tsaro kira suke yi ga jama’a da suke taimakawa wajen bada bayanai na duk wasu da basu amince da su ba, kamar yadda jami’ai ke yin kira.
Dubban rayuka ne dai suka salwanta a Najeriya, baya ga wadanda rikicin Boko Haram ya raba da gidajensu, koda yake gwamnatojin jihohin da abin ya fi shafa na cewa suna nasu kokari, kamar yadda gwamnan jihar Adamawa Sanata Muhammadu Bindow Umaru Jibrilla ya tabbar.
Domin karin bayani saurari cakakken rahotan Ibrahim Abdul’aziz.
Your browser doesn’t support HTML5