Ganin yadda yawan fashewar bom ke sanadiyar asarar rayuka hukumomi sun fara fadakar da mutane irin matakan da ya kamata su dauka idan har bom ya fashe domin su tsira da rayukansu.
Jami'in 'yansanda mai kula da warware bama-bamai na rundunar jihr Filato DSP Abel Mbibi yace yana da wuya jama'a su iya tantance bom saidai idan sun yi la'akari da wani abun da ba kasafai suke ganinshi a muhalansu ba. Idan sun ga hakan to suyi nesa dashi kana su nemi taimakon jami'an tsaro.
Mbibi yace shawarar da zasu ba mutane shi ne su dinga bincike da naura da ka iya gane abu mai hadari a jikin mutum. Kamata yayi a binciki kowane ne zai shiga wata haraba ko a kafa ko a abun hawa.
Wani sifeton 'yansanda Ezekiel Tali yace masu kira bom suna iya anfani da tukunyar da ake saka isakar dafa abinci ko wadda take anfani da firiji ko kuma galan da ake zuba mai ciki. Su kan hadasu da wayoyi domin su sarafa bom. Abu ne da zasu hada cikin dan karamin lokaci ba sai an shigo dashi daga wani wuri ba.
Idan bom ya tashi kai da bai taba ka ba kada kayi saurin gudu zuwa koina. Ka fara kwantawa a kasa domin watakila akwai wani bom din da zai biyo bayan na farkon wanda shi ne zai hallaka rayuka da dama.
Wannan fadakarwar ta biyo bayan wasu bayanai da gwamnatin tarayya ta fitar inda tace ta bankado wani shirin 'yan ta'ada na kai hare-hare tare da yin anfani da matasa maza da dabbobi kamar su awaki, shanu da rakuma. Maharan sun kuduri kai hare-haren a kasuwanni, wuraren cin abinci, wuraren cire kudi na ATM, taron gangamin siyasa da wuraren ibada.
Sanarwar ta gargadi mutane su kaucewa inda aka yi cincirindo su kuma kula da duk take-taken da basu yadda dashi ba.
Ga rahoton Zainab Babaji.
Your browser doesn’t support HTML5