Jami'an Sojin Najeriya Na Kokarin Taimakawa Amina Ali Ta Dawo Cikin Hankalinta

AMINA ALI

Jami'an sojin Najeriya na kokarin 'yar makarantar mata ta Chibok da aka ceto wadda kuma ita ce ta kasance ta farko tun lokacin da 'yan Boko Haram suka sacesu shekaru biyu da suka gabata ta komo cikin hankalinta daga dimuwar da take ciki yanzu

Amina Ali tana cikin 'yan mata kusan dari uku da kungiyar Boko Haram ta sacesu daga makarantar gwamnati ta mata dake Chibok a jihar Borno ranar 14 ga watan Afirilun 2014.

Yayinda aka sacesu wasu cikinsu sun kubuta cikin daren amma har yanzu akwai 'yan mata fiye da dari biyu da suke hannun 'yan Boko Haram. Jami'an soji da na gwamnati sun samu sun hada Amina Ali da mahaifiyarta a kauyensu wato, Mbala ranar Talata kafin sojoji su wuce dasu barikinsu.

Labarin yadda aka kubutar da Amina na cin karo da juna. Yayinda mai magana da yawun sojoji yace sun cetota ne a wani kauye da ake kira Baale kusa da Damboa su kuma 'yan Civilian JTF shugabansu Aboku Gaji cewa ya yi sun yi kacibis da yariyar ne yayin da suke yiwa 'yan Boko Haram kwantan bauna.

An dai gano Amina Ali ne da goyon 'yar yarinya da ta haifa tare da wani dan Boko Haram wanda yace shi ne mijinta. Shi dai wannan mutumin yana hannun sojoji suna cigaba da yi masa tambayoyi.

Tuni sojoji suka gabatar da Amina da diyarta da mahaifiyarta wa gwamnan jihar Borno wanda ake kyautata zaton zai kaisu wurin shugaban Najeriya Muhammad Buhari yau Alhamis a Abuja.