An samu rahoton bullowar cutar bayan daya kama wani yaro mai shekaru takwas da haihuwa, kafin kuma daga baya wani rahoto ya fito na cewa wata yarinya yar uwar yaron itama anga alamun cutar a jikinta.
Dakta Joshua Abubakar shine darektan kula da lafiyar al'ummar jihar Gombe, yayiwa wakilin Muryar Amurka Aabdulwahab Muhammad karin bayani a wata tattunawar da su kayi ta wayar tarho jim kadan bayan da suka isa kauyen.
Inda yace sun sami mutanen garin sun kuma wayar musu da kai alokacin da wata ganawa da mutanen, bayan da suka yi ma mutanen bayanin cutar ne sai wani mazaunin garin ya daga hannu yace lalle akwai ‘dan sa da yake da duk alamun da suka fada, daga nan kuma suka ‘dauki yaron zuwa Gombe, domin bashi kulawar da ta kamata.
Yanzu haka dai an dauki jinin yaron don zuwa a auna, kuma a tabbatar da cewa yana dauke wannan cuta. bayan haka dai an tura jami’an lafiya zuwa gida gida domin wayarwa da mutane kai da kuma neman wadanda ke dauke da cutar.
Ga hirar Abdulwahab Mohammed da Dakta Joshua Abubakar.
Your browser doesn’t support HTML5