Jami'an Kenya sun kama mai ginin da ya rushe ya hallaka mutane

Ginin da ya rushe

Jami’ai a kasar Kenya sun kama wanda yake da mallakar gininda ya rushe ranar Juma’ar data gabata a babban birnin kasar Nairobi, wanda ya zuwa yanzu yawan wadanda suka mutu ya kai mutane 21.

Sun ce sun kama Samuel Kamau wanda shine ke da ginin mai bene hawa 6 a matsayin gidajen zama, sun kuma ce zai bayyana a gaban kotu cikin wannan makon.

Ma’aikatan ceto sun ce sun ceto mutane da dama daga baraguzan ginin benen mai tattare da gidajen da mutane ke zaune a ciki, to sai dai ,har yanzu akwai mutane da dama da suka bace.

Ma’aikatan sun ce a halin da ake ciki har an faracire rai da sake gano wasu da ke da sauran numfashi daga karkashin rusashshen ginin. A kalla dai an ceci mutanen da suka kai 135.

Wannan bene yana wata unguwar Huruma wadda yawancin mutanenta masu karamin karfi ne ga kuma yawan jama’a. Sannan tuni dama mahukunta suka yi alla-wadai da ginin.

Ba’a san dalilin da yasa aka ki bin umarnin kauda ginin da hukuma ta bada umarni ba tuntuni. Ginin ya rushe ne sakamakon ruwan sama da ya haifar da zaftarewar kasa da ambaliya a kogin da ke unguwar.

Ginin da ya rushe