A Kenya masu aikin ceto a Nairobi babban birnin kasar suna bincike cikin baraguzan wani bene mai hawa hawa bakwai wanda ya fadi, ko da kawai wadanda suka makale da rai. Ambaliyan ruwa ne ya janyo faduwar ginin, ya danne mutane da ba'a san adadinsu ba.
Kakakin kungiyar Red Cross a kasar, Arnolda Shiundu, tace hukumomin kasar basu da masaniya kan yawan wadanda baraguzan suka danne, ta kara da cewa "suna fargabar akwai mutane masu yawa a ciki."
"Za'a yi riga malam masallaci, idan aka fara zancen wadanda suka mutu," muna ci gaba da neman mutane. Motocin aikin shigen jalpe ta iso, kuma motocin jigilar marasa lafiya ambulance duk suna nan."
Kodashike bata san yawan mutane da suke cikin ginin ba,Shiundu tace an ceto mutane 44 daga baraguzan ginin, tun bayan da ya fadi da misalin karfe 9: 30 na dare agogon kasar.
Makeken ginin yana wata unguwar marasa galihu ne mai yawan jama'a da ake kira Huruma.