Jami'an Jonathan Sun Ce Bashi da Hannu Wajen Jefawa Tambuwal Borkonon Tsohuwa

Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan.

Inji jami'an shugaba Jonathan wai bashi da hannu a argitsin da ya faru a majalisar dokokin kasar makon jiya

Jami'an na nuwa sam shugaba Jonathan bashi da hannu akan harin da 'yansandan Najeriya suka kai harabar majalisar dokokin kasar har ma suka jefawa kakakin majalisar barkonon tsohuwa.

Mai magana da yawun gwamnatin Jonatahan Doyin Okupe cewa yayi babu wata gwamnati da ta yiwa kasar aiki tun lokacin da ta samu 'yanci kamar ta Jonathan. Okupe ya mayarda martani ga abun da Obasanjo ya fada cewa gwamnatin Jonathan ta gaza.

Mutane na mayarda martani tsakanin wadanda suke ganin gwamnatin ta tabuka da wadanda suke ganin canza sheka zuwa jam'iyyar adawa ita ce mafita. Wadanda suka ce sun bar PDP domin ba zaman lafiya yaudara suke yiwa jama'a. Duk inda ake aiki shugaban kasa bai hana ba. Yin kuka da Jonathan babban kuskure ne. Abu ne kuma da ba zai haifar da alheri ba.

Babban sifeton 'yansanda Suleiman Abba bai amsa gayytar farko ta 'yan majalisa ba karkashin Barrister Usman Bello domin bada bahasi akan mamayar da 'yansanda suka yiwa majalisar dokoki.

Yayin da ake jiran zuwan sifeton ranar Laraba aka ganshi ya amsa gayyatar mataimakin shugaban kasa Namadi Sambo. To saidai ya gayawa manema labarai su dakata domin ana bincike kafin a fitar da bayani.

Ga rahoton Nasiru Adamu El-Hikaya.

Your browser doesn’t support HTML5

Jami'an Jonathan Sun Ce Bashi da Hannu Wajen Jefawa Tambuwal Borkonon Tsohuwa - 2' 25"

Amma dan APC Hamma Adama Kumo yana karfafa sauya akala. Yace abu ne da kowa ya sani a zahiri cewa PDP ta kare, ta mutu. Ya kira wadanda suka rage su yi sauri su shiga APC kafin a kulle kofa.

Dan rajin kare PDP Yusuf Lamido Cikere