Jami’an kasar Iraq sun tabattarda fashe-fashe fiye da goma sha biyu da suka ragargaza sassa daban-daban na babban birnin kasar, Baghdad, abinda ya janyo mutuwar akalla mutane sittin da uku da jikkatar wasu fiye da dari da tamanin a cikin tashin hankali mafi muni da aka share wattani ba’a ga kamar shi ba.
Wadannan hare-haren da a bisa dukkan alamu an shirya kai su daya-bayan-daya ne, sun tashi ne galibi a unguwannin ‘yan Shi’a, kuma abin na faruwa kwannaki kalilan bayan ficewar sojan Amurka daga Iraq din.
Haka kuma an kai hare-haren ne a daidai lokacinda ake zaman dar-dar tsakanin kusoshin gwamnatin kasar bayanda gwamnatin ta zargi mataimakin shugaban Iraq Tari al-Hashemida laifin kulla makarkashiyar hallaka wasu jagabannin gwamnatin.
Hashemi, wanda dan jinsin Sunni ne, ya musanta zargin da yace na siyasa ne da aka kulla mishi, inda kuma ya zargi pr-minista Nouri al-Maliki da laifin kitsa makiricin saboda, a cewar Hashemi, yana son ya kara gyara zamanshi akan karagar mulki bayan fitar sojan Amurka