Jami'an Tsaro Sun Kama Gungun 'Yan Ta'adda A Yankin Arlit Mai Iyaka Da Aljeriya

Wasu 'yan bindiga da aka kama

Jami'an tsaron Nijar karkashin runduna ta musamman da ke yaki da ayyukan ta'addanci a iyakokin kasashen Nijar da Aljeriya sun kama wasu  gungun yan ta'adda  dake aikata manyan laifuka  da suka hada da kai hare hare à wuraren hakar ma'adinai, da satar dukiyar jama'a, da tare hanyoyi.

Jami'an tsaron sun kuma kwace manyan bindigogi kirar AK 47 masu yawa a hannun 'yan ta'addan, da harsashai da kuma motoci da Babura tare da jigilar manyan bindigogi.

Runduna ta musamman na yin duk mai yiwuwa wajen gano mabuyar sauran masu aikata manyan laifuka a duk inda suke a Nijar.

makamai

Dawo da zaman lafiya a yankunan da ake fama da matsalar tsaro a Nijar shine babban burin da gwamnatin mulkin sojan Nijar ta sa a gaba a yayin wani sumame da jami’an tsaro masu yaki da 'yan tada kayar baya suka kai a maboyar 'yan ta’adda a yankin arlit dake iyaka da kasar Aljeriya gamayyar jami’an tsaron suny i nasarar kama wasu gungun 4 na yan bindiga da suke aikata manyan laifuka irinsu kai hare hare a wuraren hako ma’adinai na zinare da tare taren hanyoyi dadai sauransu.

Manyan bindigogi masu yawa ne kirar AK 47 da motoci da harsashai aka karba a hannunsu tasi’u Ibrahim shugaban rundunar jami’an tsaron 'yan sanda na yankin arlit dake iyaka da kasar Aljeriya.

Makamai

Masu fafutuka na ganin wannan al’amari a matsayin wani babban cigaba a yaki da ta’addanci a Nijar amma sukace wajibi ne hukumomi su tashi tsaye wajen karfafa matakkan yaki da y'an ta’addan domin kawo karshen ta’addanci.

Masana na ganin dole sai jami’an tsaro sun sake salon yakar 'yan ta’addan in suna son kawo karshen 'yan bindiga a kasar.

Saurari rahoton Hamid Mahmud:

Your browser doesn’t support HTML5

Jami'an Tsaro Sun Kama Gungun 4 Na Yan Ta'adda À Yankin Arlit Mai Iyaka Da Kasar Aljeriya