An Sake Yunkurin Hallaka Trump - FBI

Dan takarar shugaban kasa Donald Trump na jam'iyyar Republican

Lamarin ya faru ne kusan watanni biyu bayan wani yunkurin hallaka Trump a wani gangamin yakin neman zabe a jihar Pennsylvania.

Jami'an Tsaro na Sirri a Amurka sun bude wuta bayan ganin wani mutum dauke da bindiga kusa da filin wasan kwallon lambu (golf) na tsohon shugaban Amurka Donald Trump da da ke yankin West Palm Beach a jihar Florida.

Lamarin ya faru ne a ranar Lahadi yayin da dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Republican yake yin wasan kwallon na golf.

Babu wani rahoto da ke nuna wani ya ji rauni.

Trump a filin wasan golf

Wasu jami’an Amurka biyu ne suka tabbatar wa da Kamfanin Dillancin labarai AP aukuwar lamarin.

Jami'an sun ce mutumin ya gudu a cikin wata mota kirar SUV amma daga bisani an kama shi a wata karamar hukuma kusa da wurin da jami'an tsaron yankin suka cafke shi.

Jami'an sun ce ba a ba su da izinin tattauna batun a bainar jama'a ba, kuma sun yi magana ne bisa sharadin boye sunansu.

Hukumar binciken manyan laifuka ta FBI ta ce ga dukkan alamu, Trump aka hara a yunkurin kai harin.

Yadda 'yan sanda suke karkata akalar tafiyar motoci bayan yunkurin harin

FBI ta bayyana Ryan Wesley Routh a matsayin mutumin da ake zargi da yunkurin kai harin kamar yadda AP ya ruwaito.

Lamarin ya faru ne kusan watanni biyu bayan wani yunkurin hallaka Trump a wani gangamin yakin neman zabe a Pennsylvania.

An samu bindiga kirar AK a wurin da lamarin ya faru kusa da filin wasan golf na Trump, kamar yadda aka shaida wa AP.