Jami'an Tsaro Sun Fara Samun Bayanan Sirri Daga 'Yan Kasa A Nijer

Shugaban Nijar Bazoum Mohamed

Rundunar hadin gwiwar G5 Sahel ta sanar da samun nasarar kama wasu ‘yan ta’adda sama da 10 a yankin iyakokin kasashen Nijer, Burkina, Faso da Mali bayan da ta bi diddigin wasu bayanan da ta samu daga al’ummar kauyukan jihar Tilabery.

Masu fafutuka suna ganin wannan al’amari a matsayin wani babban ci gaba a yaki da ta’addanci amma kuma suka ce wajibi ne hukumomi su dauki matakin kare duk wanda ya ke tsegunta bayanai na sirri.

A sanarwar da ta fitar a jiya Talata rundunar hadin gwiwar G5 Sahel ta ce sakamakon wasu bayanan da wata bataliyar sojojin Nijer da ke da sansani a kauyen Wanzarbe na gundumar Tera ta samu daga mazauna kauyen Balley Koira sun bada damar cafke wasu ‘yan ta’adda 9 dauke da shanu 18 da babur 1 sabo ful da suke shirin batarwa a kasuwar kauyen na Balley Koira dake a tazarar km 30 a kudu maso gabashin Wanzarbe.

Wannan wata alama ce dake nunin an fara samin canjin tunani a wajen al’umar yankin da wani lokaci ake zargi da hada kai da ‘yan ta’adda inji wani mai bin diddigin al’amuran yau da kullum Ibrahim Kantama.

Haka kuma a ranar 15 ga watan Satumba jandarmomi a kauyen Yatakala dake kilomita 3 da Wanzarbe sun damke wani mai yi wa ‘yan ta’adda aikin leken asiri bayan da aka sanar da su ta wayar tarho. Mamba a kungiyar ‘yan jarida masu kula da sha’anin tsaro AbdoulRzak Ibrahima, ya ce alama ce dake nunin tafiya ta kama hanya a game da yunkurin murkushe ‘yan ta’adda a yankin Tilabery.

Yanzu haka wadannan ‘yan bindiga kimanin 10 da shanu 18 da babur din da aka kama a hannunsu na can tsare a cibiyar yaki da ta’adanci . Cikin irin wannan yanayi daukar matakai, bayar da kariya ga masu kwarmata bayanai ga jami’an tsaro wani abu ne da ya zamewa hukumomi wajibi a cewar masharhanta.

Wani labarin na daban na cewa jami’an tsaron Jandarman gundumar Gidan Roumji a jihar Maradi sun kama bindigogi kirar AK 47 kimanin 10 da harsasai 8200 bayan kaddamar da samame a wasu kauyuka 4 abin da tuni ya rutsa da wasu mutane da ake zargi da hannu a wannan

Ga rahoton Souley Moumouni Barma daga birnin Yamai:

Your browser doesn’t support HTML5

Sanarwar Rundunar G5 Sahel