ABUJA, NIGERIA - Jami’an na EFCC sun yi wa gidan tsohon gwamnan na kogi kawanya ne da sanyin safiyar Laraba, inda wadanda suka shaida da idanun su suka bayanna yadda jami’an EFCC suka tare hanyar shiga harabar gidan, kamar yadda manyan jaridun gida na Najeriya suka rawaito.
Wannan farmakin ya zo ne biyo bayan zarge-zargen da ake yi wa Bello, musamman dangane da karkatar da wasu kudade da aka yi kiyasin sun kai Naira biliyan 100 a lokacin da yake gwamna, zarge-zargen da suka fito a watan da ya gabata, amma dai Bello ya musanta hakan.
A tsakiyar watan Maris ne EFCC ta gurfanar da Bello a gaban kotu bisa zargin karkatar da wasu kudade tun daga watan Satumban 2015, kafin hawansa kujerar gwamna. Shari’ar da ta biyo baya, karkashin jagorancin mai shari’a James Omotoso na babbar kotun tarayya da ke Abuja, amma dai tsohon gwmanan da lauyoyinsa sun musanta haka.
Wannan diran mikiya da Hukumar EFCC tayi a gidan Yahaya Bello ya janyo cece kuce, inda ofishin yada labaransa ya yi Allah wadai da abin da EFCC ta yi.
Suna masu cewa irin wannan yunkuri ya sabawa dokar da kotun shari’a ta kasa reshen Lokoja ta bayar, wanda ya haramta cin zarafi, kamawa, ko gurfanar da Bello gabanin yanke hukunci kan shari’ar da ake yi.
Dangane da abin da ke faruwa, ofishin yada labarai na Bello ya yi kira ga shugaban kasa Bola Tinubu da ya sa baki, inda ya bukaci hukumar EFCC ta bi ka’idojin doka da kuma mutunta doka. Sun bayyana cewa abin da EFCC ta yi na nuna rashin mutunta tsarin da ya dace.
-Yusuf Aminu Yusuf