Jami’ai A Pakistan Sun Toshe Hanyoyin Shafukan Sadarwa Da Hawa Yanar Gizo

Salula

Jami’ai a Pakistan sun haifar da cikas ga hawa yanar gizo da toshe kafar shafukan sadarwar zamani a kasar baki daya a yammacin jiya Lahadi.

WASHINGTON, D. C. - Haka ya zo ne a dai-dai lokacin da jam’iyar daurarren tsohon Firai Ministar kasar Imran Khan, ke kaddamar da gangamin fitar da manufofi da tara kudaden ta, ta kafafen sadarwar zamani, a shirye-shiryen zaben da ake shirin gudanarwa a wata mai zuwa.

PAKISTAN-KHAN

An shirya gudanar da babban gangamin a kasa baki daya, da niyyar tsallake shingen da gwamnati ta gitta na ganin ta dakile taron jama’iyar ta Tahreek-e-Insaf ko PTI.

Wata kuri’ar ra’ayin jama’a da aka kada ta nuna cewa, jam’iyar ita ce mafi karfi a fagen siyasar kasar, yayin da tsohon Firai Ministan kasar, Imran Khan ya kasance mafi farin jinni.

Wata kungiyar mai zaman kanta NetBlocks, dake sa ido kan cigaban hakkokin kafofin sadarwar yanar gizo, da tsaron su, dama yadda ake gudanar dasu, da jami’an PTI sun tabbatar da tsaikon a tashin farko, lokacin da ake gudanar da taron gangamin akan shafukan yanar gizo.