Jamhuriyar Nijer da Jamhuriyar Benin sun kulla yarjejeniyar ayyukan soja wace a karkashinta dakarun kasashen biyu zasu yi aikin hadin gwiwa a wannan lokaci da bayanai ke nuna cewa kungiyoyin ta’addancin yankin Sahel sun fara yada ayyukansu zuwa kasashen gabar teku.
A karshen wata tattaunawar da aka shafe wunin Litinin ana gudanarwa a nan Yamai a karkashin jagorancin Ministan Tsaron Nijer, Alkassoum Indatou da takwaran aikinsa na Benin, Dr Mouatin Fortuney Alain tawagogin kasashen biyu suka cimma wannan yarjejeniya wa ce a karkashinta zasu tinkari kungiyoyin ta’addancin da ke kokarin yada ayyukansu a baki dayan kasashen yammacin Afurka kamar yadda a yanzu haka suka fara kai farmaki a kasashen gabar teku.
Ya ce tun da wuri muka gano cewa samun galabar wannan yaki da ‘yan takife abu ne da ke bukatar hadin gwiwar kasashen yankin baki daya amma kuma wajibi ne a karfafa wannan mataki da yarjejeniyar kasa da kasa. Idan aka dubi kasashen da ke fama da wannan matsala a yankin Sahel Nijer tafi kowace kasa nuna juriya. Can dama Nijer ta sha taimaka mana da bayanan sirri daga sojan samanta shi ya sa muka ga dacewar mu kulla yarjejeniyar a tsakanin hukumomin tsaron Nijer da Benin, ga shi kuma abin ya tabbata a yau.
Jamhuriyar Benin mai makwabtaka da Nijer ta bangaren kudu maso yammaci na matsayin tashar jirgin Ruwa mafi kusa da Nijer saboda haka galibin kayayyakin dake shigowa ko fita daga kasar kan bi ta wannan gaba kuma yanzu haka kasashen biyu na gudanar da ayyukan shimfida bututun man da zai dangana da tekun Atlantika da nufin shigar da shi a kasuwannin duniya saboda haka gwamnatin Nijer a shirye take ta tallafa wa Benin da dukkan abubuwan da take bukata domin tunkarar kalubalen dake gabanta inji Ministan Tsaro, Alkassoum Indatou.
Ya ce idan a yau makwabtanmu na Benin na bukatar tallafi a shirye muke domin yin haka nauyi ne da ya rataya a wuyarmu , idan makwabtanmu na Burkina ma suka bukaci mu taimaka masu to ba zamu yi kasa a gwiwa ba saboda ba ma fatan wata kasa ta fuskanci abin da ya taba samun mu a Inates ko a Chinagoder saboda haka Nijer na shirye ta yi duk mai yiyuwa don taimaka wa sauran kasashe su tsaya da kafafunsu.
To ko ya masana ke kallon wannan yunkuri na Nijer da Benin? Abdourhamane Alkassoum mai sharhi akan sha’anin tsaro ya yi tsokaci.
A watan Disamban 2021 ne aka kai harin ta’addanci na farko a Jamhuriyar Benin, kuma tun daga wancan lokaci an yi ta fuskantar wasu hare haren na daban akan iyakarta da Burkina Faso, abin da ke gaskanta hasashen masana cewa kungiyoyin ta’addancin Sahel na da gurin yada ayyukansu a baki dayan Afurka ta Yamma.
Saurari rahoton Souleyman Barma:
Your browser doesn’t support HTML5