An gurfanar da Malam Nuhu Arzika da Musa Tangari a gaban babban kotun Niamey bisa ga zargin cewa suna cikin kungiyar Boko Haram.
Malam Mustapha Kadi wani shugaban kungiyar farar hula a Niamey ya zanta da wakilin Muryar Amurka akan kamun da aka yi.Yace suna jiran su ji abun da alkali zai yanke ko ya fada.Su ma alkalan kotun suna shawara akan abun da zasu yi yayinda da 'yan sanda suke famar tare mutane da suka yi dafifi a harabar kotun.
Malam Kadi yace hankalin mutane ya tashi kuma 'yansanda suna tsoron za'a yi tarzoma domin jama'a na cewa sharri ne aka yiwa shugabannin. Babu gaskiya a cikin zargin. Jama'a suna cewa gwamnati ta dawo kan hanyar gaskiya.
Jama'a na ganin an kama shigabannin ne domin sun fadi albarkacin bakinsu. Malam Kadi yace babu yadda za'a yi dan kungiyar farar hula ya shiga kungiya Boko Haram. Yace su abun da suke nema a Nijar shi ne zaman lafiya kuma kasarsu ta cigaba.
Gwamnati ta kamasu ne domin bata son Nuhu Arzika da Musa Tangari. Yace gwamnati mai ci a kasar bata son ana fitowa ana fadin gaskiya. Wanda ya rantse da Kur'ani ya kamata ya tsare gaskiya.
Ga karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5