Yau asabar ake gudanar da zaben shugaban kasa zagaye na biyu a jamhuriyar Niger dake yammacin Afrika, domin maida kasar karkashin mulkin damokaradiya bayan hambare gwamnatin shugaba Mamadou Tandja da aka yi bara a wani juyin mulkin soji. Muhammadu Issoufou na jam’iyar PNDS Tarayya ne ya sami ranjaye a zaben da aka gudanar ranar 31 ga watan janairu da kashi talatin da shida bisa dari na kuri’un yayinda Saini Oumarou na jam’iyar MSD Nasara ya sami kashi ishirin da uku. Mr. Issouf ne yake da kyakkyawan karbuwa zaben da za a kada yau, bayan ya samun goyon bayan mutane hudu daga cikin wadanda suka tsaya takara a zagayen farko. A lokacin da yake yakin neman zabe, Mr. Issoufou yace lokaci ya yi da za a yi canji a Niger, yayinda Mr. Omarou ya yi alkawarin ci gaba da ayyukan da Mr. Tandja ya fara zamanin mulkinsa na shekaru goma. Mr. Oumarou ya kuma yi alkawarin sakin tsohon shugaban kasar idan aka zabe shi, wanda yanzu yake tsare bisa zargin rubda ciki da dukiyar talakawa
Yau asabar ake gudanar da zaben shugaban kasa zagaye na biyu a jamhuriyar Niger dake yammacin Afrika.