Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Alassane Ouattara yace wani kwamiti yace shine halaatacen shugaban Ivory Coast.

Wounded men receive medical care at a hospital in Abidjan's Treichville neighborhood on March 8, 2011
Wounded men receive medical care at a hospital in Abidjan's Treichville neighborhood on March 8, 2011

Shugaban kasar Ivory Coast da duniya ta yi na’am da shi, Alassane Ouattara ya samu karin karfin guiwa sosai jiya alhamis, a bayanda ya bayyana cewa wani kwamitin shugabannin kungiyar kasashen Afrika ta ayyana cewa shi ne halaltaccen shugaban kasar Ivory Coast, ta kuma bayarda umurnin cewa a rantsar da shi ba tare da jinkiri ba. Alassane Ouattara yace sun yi ganawa mai amfani da kwamitin shugabannin kasashe kungiyar kasashen Afrika, kuma sun sake jaddada cewa shi ne shugaban da al’ummar Ivory Coast suka zaba.

Wannan shine hukumcinsu na karshe kan wannan batu, saboda haka babu yadda za a sauya shi. Amma kuma sun roke shi cewa domin a tabbatar da kawo sasantawa a tsakanin al’ummar kasar, ya kafa gwamnatin da zata kunshi sauran jam’iyyu da kungiyoyin al’umma, ya kuma yi kokarin samo hanyar da Laurent Gbagbo zai bi ya sauka da mutuncinsa. MDD ta tabbatar da Mr. Ouattara a zaman wanda ya lashe zaben shugaban kasa na watan nuwamba amma Mr. Gbagbo ya ki sauka ya mika masa mulki.

Mr. Gbagbo bai halarci taron na jiya alhamis a Addis Ababa ba, amma nan take wakilinsa a can ya ce ba su yarda da wannan shawara ba. A can Ivory Coast din, gwamnatin Gbagbo ta ce ba ma zata yarda jirgin Mr. Ouattara, wanda ya halarci taron na jiya, ya sauka idan ya koma kasar ba. Ba a dai san yadda kungiyar kasashen Afrika zata sanya Mr. Gbagbo yayi aiki da wannan umurni nata ba. Amma kuma, kwamishinan zaman lafiya da tsaro na Kungiyar, Ramtane Lamamra, yace sun riga sun fada ma Gbagbo cewa ya san inda dare yayi masa, kuma tilas za a yi aiki da wannan umurni na shugabannin.

Yace ba zasu yarda da a’a ba. Su ma mutane ne masu taurin kai, kuma zasu ci gaba da kokari tukuru kan wannan batun. Sun yi imanin cewa sassan na kasar Ivory Coast ba zasu yarda su kyale kasarsu ta sake fadawa cikin yakin basasa ba. babu wani shugaba mai hankali da zai yarda ya dauki nauyin wannan mummunan hali.

XS
SM
MD
LG