Daukan matakan sun biyo bayan bayyanar cutar ne a wasu kasashen Afirka dake da dangantaka ta kud da kud da kasar ta Niger musamman ma tarayyar Najeriya.
A safiyar jiya ne ministan kiwon lafiya na kasar Mani Agali yayi hadin gwiwa da babban mai shiga tsakani ta kasar ta Niger Shehu Ahmadu. Tare suka kai wata ziyara a wasu wurare domin gane ma idanunsu yadda binciken yake gudana.
A filin saukar jirgin sama dake Niamey duk wasu matakan bincike an daukesu. Da zara mutum ya sauka daga jirgin sama jami'an zasu tambayeshi sunashi daga inda ya fito da kuma inda zashi. Idan mutum na tari ko yana da masassara ko ciwon kai sai a wareshi gefe guda.
Kawo yanzu babu wani dan kasar da ya kamu da cutar amma sun dauki shirin ne saboda kare kasar da al'ummarta daga mummunar cutar mai kisa da gaggawa fiye da kima.
Ga rahoton Abdullahi Mamman Ahmadu.
Your browser doesn’t support HTML5