Jamhuriyar Niger ta Dauki Matakan Kare Kasar daga Cutar Ebola

Shugaba Mahamadou Issoufou na Jamhuriyar Nijar

Ministan kiwon lafiyar kasar Niger Malam Manu Agalu ya bayyana irin matakan kariya da suke dauka idan mutane sun fito daga kasashen da cutar ebola ta bulla.

Bayan binciken lafiyar mutane da ake yi a filayen saukar jiragen sama akwai wasu matakan kariya masu karfi da gwamnatin kasar ta dauka kamar binciken lafiyar mutane dake shige da fice daga kasashen dake makwaftaka da ita.

Jihar Kwanni na cikin jihohin dake makwaftaka da tarayyar Najeriya inda matakan suka kasance na bai daya tsakanin kasashen biyu, wato Najeriya da Jamhuriyar Niger.

Wani Malam Zakari ma'aikacin kiwon lafiya daga Najeriya yana aiki akan iyakar kasar da Niger. Yayi bayanin naurar da yake aiki da ita wadda yake gwada mutane da suka ketaro daga Niger kafin su shiga kasar ko kuma suna fita daga kasar kafin su tsallaka zuwa cikin Niger.

Wadanda aka gwadasu sun bayyana yadda suka ji. Ibrahim Umaru da aka gwada yace ya ji dadi domin yanzu ya san yana da lafiya babu abun damuwa.

Kodayake cutar bata bulla ba a Jamhuriyar Niger, matakan da gwamnati ke dauka ya taimaka kwarai musamman wajen rage fargaban 'yan kasar.

Ga rahoton Abdullahi Manman Ahmadu.

Your browser doesn’t support HTML5

Jamhuriyar Niger ta Dauki Matakan Kare Kasar daga Cutar Ebola -3' 34"