Jama'a Sun yi Barka da Rashin Tsadar Kayayyaki Bana

Musulmai a Najeriya da ma wasu sassa a duniya suna azumi a wannan wata mai tsarki na Ramadan da kama baki daga daren assubahi zuwa magariba.

Kayayyakin masarufi basuyi tashi gwauron zabo ba kamar yanda a wasu lokuta yake faruwa a lokacin watan Azumi.

Ya zuwa yanzu daidai lokacin da watan Azumi Ramadan ya raba biyu magidanta a garin Kaduna, da Kewaye na barka dangane da yanda farashin abinci da sauran kayayyakin masarufi basuyi tashi gwauron zabo ba kamar yanda a wasu lokuta yake faruwa a lokacin watan Azumi.

Jama’a da wakilimu ya zanta dasu sun danganta rashin tashi kayayyakin da rashi kudi a hannun jama’a.

Ganin watan Azumin ya raba yanzu hankalin ya karkata kan yanda za’a yiwa Iyali dinkin kayan sallah.

Wasu masu sayarda yadudduka da kuma balawus sunce suma a bana basu sayi harjarsu da tsada ba.

Jama'a Sun yi Barka da Rashin Tsadar Kayayyaki Bana - 2'50"