Jam'iyyar RPP a Nijar Ta Tsaida Alma Oumarou Takarar Shugaban Kasa

Alma Oumarou

A jamhuriyar Nijar ‘yan takarar zaben shugaban kasa na ci gaba da kunno kai a yayin da ya rage watanni 3 kacal ayi zaben kasar. 

A karshen makon da ya gabata ne sabuwar jam’iyyar RPP Farilla ta bayyana Alma Oumarou, wani mashawarcin Shugaba Issouhou Mahamadou a matsayin wanda zai wakilceta a zaben ranar 27 ga watan Disamba.

Tawagogin magoya bayan jam’iyyar RPP da suka fito daga yankuna 8 na jamhuriyar Nijar suka hallara a babban taron da uwar jam’iyyar ta kira da nufin tattauna matsayin su game da zabubbukan da ke tafe.

Dan majalisar dokokin kasa Chitou Maman, na daga cikin shugabanin jam’iyya RPP, ya ce sun kira wannan babban taron jam’iyyar ta su ne domin sun duba ka’idojin da jam’iyyar ta shata don tabbatar da dan takarar Shugaban kasa da kuma sauran ‘yan takarar da za su yi wa jam’iyyar takara a zaben da ke tafe.

Babban taron ya bayyana shugaban jam’iyyar RPP, Alma Oumarou a matsayin wanda zai tsaya mata a zaben shugaban kasa.

A lokacin da yake jawabi jim kadan bayan taron, Alma Oumarou ya ce ya amince ya tsaya wa jam’iyyarsa takarar shugaban kasa kuma babu gudu babu ja da baya, sannan ya yi kira ga masu zabe da su guji karbar kudi domin su zabi wani dan takarar.

Oumarou ya sha alwashin kwatanta adalci a tsakaninsa da abokan tafiyarsa na jam’iyyar RPP duba da abubuwan da ke faruwa a jam’iyyu da dama a yanzu haka a Nijar.

A watannin da suka gabata ne aka kafa RPP Farilla bayan wani rikicin shugabanci da ya barke a jam’iyyar MPR Jamhuriya.

Alma Oumarou na daga cikin manyan kusoshin jam’iyyar MNSD NASARA a zamanin shugaba Tanja Mamadou inda ya sha rike mukamin minista.

A halin yanzu, ya na daga cikin mashawartan shugaban kasar Nijar Issouhou Mahamadou a fannin kasuwancin kasa da kasa.

Saurari cikakken rahoton Souley Moumouni Barma:

Your browser doesn’t support HTML5

Jam'iyyar RPP a Nijar Ta Tsaida Alma Oumarou Takarar Shugaban Kasa