A jamhuriyar Nijer, jam’iyyar PNDS Tarayya mai mulki ta bayyana goyon bayanta ga binciken da aka gudanar domin tantance hanyoyin da aka bi da wasu dubban miliyoyin CFA da suka salwanta a ma’aikatar tsaron kasar, sai dai jam’iyyar tace ta gano wasu ‘yan kasar na amfani da wannan dama don goga mata kashin kaji. Zargin da ‘yan adawa ke ganin sa a matsayin salo irin na wanda ya rasa tudun dafawa.
Zazzafar mahawarar da ta biyo bayan binciken da ya rutsa da wasu manyan jami’ai da ‘yan kasuwa masu alaka da jam’iyyar PNDS Tarayya ita ce ta sa shugabannin jam’iyyar mai mulki gaggauta fitar da sanarwar domin bayyana matsayinta a hukunce kamar yadda shugaban matasan jam’iyyar Daoui Ahmed Baringaye ya bayyana.
To sai dai Alhaji Doudou Mahamadou na jam’iyyar adawa ta RDR Canji na cewa idan aka nazarci wannan sanarwa, za a gane cewa jam’iyyar PNDS Tarayya ta kwance wa kanta zane a kasuwa ne.
A baya bayan nan Kungiyar alkalan shari’a da ta lauyoyi sun bukaci gwamnatin kasar ta gabatar da wannan batu gaban shari’a don hukunta masu hannu a wannan ta’asa ta ofishin ministan tsaro, to amma jam’iyyar PNDS a sanarwar ta tace akwai wata boyeyiyar manufa a tattare da wannan bukata.
Saurari cikakken rahoton cikin sauti.
Your browser doesn’t support HTML5