Jam’iyyar PDP mai adawa a Najeriya ta zargi gwamnatin APC da gazawa wajen kawar da ‘yan bindiga da suka addabi jihar Neja dake Arewa maso tsakiyar kasar.
Jihar Nejan dai na daya daga cikin jihohin Arewacin Nigeria dake shan bakar azabar ‘yan bindiga da tuni gwamnatin Najeriya ta ayyansu a matsayin ‘yan ta’adda.
A wani taron masu ruwa da tsaki na jam’iyyar ta PDP da ta gudanar a Minna fadar gwamnatin, Jihar Nejan ta ce gwamnatin APC ta gaza matuka wajen yaki ko kuma fatattakar ‘yan ta’addan dake cin karensu babu babbaka a jihar, a cewar shugaban PDP na yankin gabashin Jihar Hon. Haruna Labaran.
Shi ma dai shugaban PDP na jihar Nejan Barista Tanko Beji, ya ce yanzu sun bankado wani shiri da gwamnatin APC ke shirin yi na yin amfani da yankunan da ‘yan fashin dajin suka kori jama’a domin tabka magudi a lokacin babban zabe na shekarar badi.
Ku Duba Wannan Ma Rikicin APC A Kano: Bangaren Shekarau Zai Daukaka Kara a Kotun KoliTuni dai Jam’iyyar ta APC ta mai da martini akan wannan zargi na PDP, jami’in hulda da jama’a na Jam’iyyar APC a jihar Nejan Alhaji Musa Sarkin Kaji ya ce zargi ne kawai irin na ‘yan adawa, amma maganar tsaro ba a wasa da shi domin ya shafi kowa.
A yanzu haka dai rahotanni sun nuna cewa dubban ‘yan gudun hijira ne suka cika sansanin ‘yan gudun hijirar da ‘yan ta’addan dajin suka tarwatsa a garuruwan kontagora da kuma Gwada ta yankin shiroro.
Saurari rahoto cikin sauti daga Mustapha Nasiru Batsari:
Your browser doesn’t support HTML5