A zaman kotun da aka yi ranar Laraba ta kafar sadarwa ta zamani ta Zoom, alkalan kotun sun soke jimlar kuri’u 165,663 daga cikin adadin kuri’un da gwamna Abba Kabir Yusuf ya samu a zaben ranar 18 ga watan Maris da ya gabata.
Dalili kuwa wadancan kuri’un an gano cewa na bogi ne a cewar kotun, a don haka sai kotun ta bada umarni ga hukumar zabe ta mika takardar cin zabe ga Alhaji Nasiru Yusuf Gawuna na jam’iyyar APC saboda shi ke da kuri’u mafiya rinjaye.
Barrister M.A Lawan, wanda ya jagoranci lauyoyi da suka kare jam’iyyar APC a gaban kotu a yayin shari’ar, ya ce kotu ta yarda da hujjojin da suka gabatar.
“Mun gabatar da shaidu da hujjoji kuma kotu ta gamsu da wadannan hujjoji namu, hakan ta sanya muka yi nasara a kotu,” a cewar Lawan.”
Sai dai Barrister Bashir Yusuf Muhammad Tudun Wuzirci, daya daga cikin lauyoyin da suka wakilci jam’iyyar NNPP da Abba Kabir Yusuf a gaban kotun na cewa, hukuncin da aka yanke na cike da bam mamaki, amma akwai kutuna na gaba.
“Za mu tuntubi wadanda muka kare, zamu tattauna dasu kuma babu shakka zamu daukaka kara domin ba mu gamsu da wannan hukunci ba.”
Yanzu haka dai birni da kewayen Kano na cikin kulawar tsauraran matakan tsaro, a daidai lokacin da magoya bayan wadanda suka yi nasara a zaben ke ci gaba da murnar nasarar shari’a.
Sai dai wata sanarwa da hukumar 'yan sanda a Kano ta fitar ta ce hukumomin tsaro a Kano sun sanya dokar takaita zirga-zirgar jama'a tsawon sa'o'i 24 a birni da kewayen Kano, a don haka rundunar ta bukaci al'umar jihar su kiyaye doka da oda domin wanzar da zaman lafiya a jihar.
Your browser doesn’t support HTML5