Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Magoya Bayan APC Sun Yi Tattaki Zuwa Ofishin INEC A Kano


Dan takarar jam'iyyar APC mai mulki a Kano, Nasiru Gawuna
Dan takarar jam'iyyar APC mai mulki a Kano, Nasiru Gawuna

A farkon makon nan hukumar INEC ta ayyana dan takarar NNPP, Abba Kabir Yusuf, wanda aka fi sani da Abba Gida-gida, a matsayin wanda ya lashe zaben Gwamna a jihar, wanda aka yi a ranar 18 ga watan Maris a Najeriya.

Magoya bayan jam’iyyar APC mai mulki a Kano, sun yi tattaki zuwa ofishin hukumar zabe ta INEC, don nuna rashin gamsuwarsu da sakamakon zaben gwamna.

A farkon makon nan hukumar ta INEC ta ayyana dan takarar NNPP, Abba Kabir Yusuf, wanda aka fi sani da Abba Gida-gida, a matsayin wanda ya lashe zaben Gwamna a jihar, wanda aka yi a ranar 18 ga watan Maris a Najeriya.

Rahotanni sun yi nuni da cewa, yayin tattakin, an ga magoya bayan dan takarar APC, Nasiru Gawuna dauke da kwalaye da aka yi rubutu iri-iri suna waka suna dosar ofishin na INEC.

“Zaben jihar Kano bai kammalu ba,” wani daga cikin masu tattakin ya ce a wani hoton bidiyo da gidan Rediyon Freedom ta watsa kai-tsaye a shafinsa na Facebook.

Hukumar INEC ta ce Abba na NNPP ya samu kuri’a 1,019, 602 yayin da Gawuna ya samu 890,705.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG