Dubban magoya bayan jam’iyyar Moden Lumana da suka fito daga ciki da wajen Nijar ne suka hallara a garin Dosso inda suka gudanar da babban taron jam’iyyar domin tattauna al’amuran da suka shafi sha’anin zabe inda mahalarta taron suka sake jaddada tsohon Firai Minista Hama Amadou a matsayin dan takarar zaben shugaban kasa.
Alhaji Laouali Salissou Leger na daga cikin wadanda suka halarci wannan taro, ya ce duk abin da aka saka a siyasa to a siyasance ake daukar shi kuma tabbas a cikin jam’iyyasu wanda suke buri kuma ‘yan kasa ke buri ya zama dan takara shi ne Hama Amadou.
A lokacin da yake jawabin amincewa da takarar, Hama Amadou, ya yi kira ga magoya bayansa da su tashi tsaye don ganin Moden Lumana ta yi nasarar kawar da PNDS Tarayya daga karagar mulki.
Hama Amadou na daga cikin mutanen da kotu ta yi wa daurin shekara 1 a gidan yari saboda samun su da laifin sayen jarirai, saboda haka ake ganin a dokace ba shi da ‘yancin shugabancin jam’iyya ballantana shiga zabe.
“Ba za’a iya hana ni morar ‘yancina na dan kasa ba saboda iyayena dukkansu haifaffun Nijar ne,” abinda Hama Amadou ya fada kenan a cikin harshen Zabarmanci.
Kakakin jam’iyyar PNDS Tarayya Assoumana Mahamadou, ya ce batun cancantar shiga zabe ko rashinsa wata magana ce da ta shafi kotun tsarin mulkin kasa.
Wannan zama da ya bai wa Hama Amadou tikitin zabe a Dosso ya gudana ne kwana daya bayan da wata kotun birnin Yamai ta bai wa uwar jam’iyya izinin ta shirya taro bayan da shugaban rikon kwarya na jam’iyyar ta Moden Lumana Oumarou Noma ya shigar da kara a bisa korafinn cewa shi ke da hurumin shirya irin wannan taro.
Saurari cikakken rahoton Souley Moumouni Barma:
Your browser doesn’t support HTML5