Kalaman uban jam’iyyar APC Bola Ahmed Tinubu da ke nuna shi ya taimaka wa shugaba Buhari ya yi nasara a zaben shekarar 2015, ya sa wasu da ke neman damar yi masa zarra ko kawar da shi daga takara cewa bai cancanci samun tikiti ba.
Dan kwamitin mara baya ga shugaba Buhari Ibrahim Musa, ya ce ya zama wajibi Tinubu ya nemi afuwar shugaba Buhari da jam'iyyar APC akan kalaman.
Shi ko marubuci a jaridar Leadership Hayatu Muhammad Hussaini, cewa ya yi fidda dan takara daga arewa don ya fafata da Atiku shi ya zai dace a jam'iyyar APC duba da cewa 'yan kudu maso yammaci da gabashin kasar basu hada kansu ba.
A nasa bangaren, Sanata Abu Ibrahim ya ce mafi adalci shi ne mulki ya koma kudu.
Tuni dai dandalin Eagle Square da ke birnin tarayya Abuja inda za a gudanar da zaben fidda gwanin jam'iyyar APC ranar Litinin ya dau harama.
Shugaban kwamitin tantance ‘yan takara na APC John Odigie Oyegun ya ce cikin ‘yan takara 23, 22 sun amince su janye don samun dan takara daya ta hanyar daidaitawa, amma daya daga ciki bai amince ba ya bukaci a gudanar da zabe sai dai in shi za a tsayar. Ana rade-radin Bola Tinubu ne wanda ya ki amincewa da matakin.
Saurari cikakken rahoton cikin sauti:
Your browser doesn’t support HTML5