Jam'iyya Mai Mulki a Venezuela Na Ikirarin Lashe Zaben 'Yan Majalisar Kasar

'Yan Adawa sun kauracewa zaben majalisar dokokin Venezuela bayan da suka yi zargin an tafka magudi.

Shugaban kasar Venezuela Nicolas Maduro na jam’iyyar Socialist Political Alliance na ikirarin samun nasara a zaben majalisar dokokin kasar da aka yi a ranar Lahadi 6 ga watan Disamba, kuma ya na shirin samun ikon Majalisar Dokokin kasar, reshen gwamnatin na karshe da ‘yan adawa su ka fi rinjaye.

'Yan takarar magoya bayan Maduro sun sami kashi 67 cikin 100 na kuri'un da aka kada, a cewar kwamitin hukumar zabe ta kasar, yayin da wadanda su ka jefa kuri'a yawansu ya dan zarta kashi 30 cikin 100.

'Yan adawar sun zargi Maduro da tafka magudi a zaben tare da yin kira ga magoya bayansu da su kauracewa zaben .

Fiye da kasashe 50, ciki har da Amurka, ba su amince da Maduro a matsayin shugaban Venezuela ba, maimakon haka sun amince da Guaido a matsayin shugaban kasar ta Venezulea da ke kudancin yankin Amurka.