Jam'iyar MPR A Nijer Ta Ce Zata Tsaya Takara A Zabukan 2020 Da 2021

MPR

Shugaban jam’iyyar Albade Abouba ya ce jam’iyyar MPR a jamhuriyar ta shirya domin shiga zabukan dake tafe a kowanne mataki, wato na kansiloli, da ‘yan majalisar dokoki, da kuma shugaban kasa

Dubun dubatar magoya bayan jam’iyyar MPR a jamhuriyar Nijer ne suka hallara a dakin taron Palais du 29 juillet dake birnin Yamai domin murnar cika shekaru 4 da kafa wannan jam’iyya wacce a yau ke a matsayi na 4 ta bangaren wakilci a majalisar dokokin Nijer, yayinda a dayan bangaren bikin ya kasance wani lokacin fayyace kudurorin da jam’iyyar ta sa gaba, musamman akan maganar zaben dake tafe.

Shugaban jam’iyyar Albade Abouba ya ce jam’iyyar MPR a jamhuriyar ta shirya domin shiga zabukan dake tafe a kowanne mataki, wato na kansiloli, da ‘yan majalisar dokoki, da kuma shugaban kasa. Saboda haka babban taron jam’iyyar na gaba, za su tsayar da komai a game da wannan kudiri.

Jam’iyyar MPR a Nijer ta yi mubaya’a ga dan takarar PNDS Tarayya Issouhou Mahamadou a zaben shekarar 2016 tun a zagayen farko. Saboda haka, fidda sanarwar shigar jam’iyyar sahun masu zawarcin kujerar shugaban kasa ke daukar hankalin jama’a,

Mataimakin shugaban jam’iyyar MPR, Alhaji Alma Oumarou shi ma ya jaddada ya cewa wannan karon jam’iyyar zata fidda dan takara a zaben shekarar 2020 da na 2021 da ake shirin yi a kasar.

Matasa da mata su suka fi rinjaye a yawan al’ummar Nijer, dalilin da ya sa shugabar matan MPR Mme Lamido Salamatou Bala Goga, ke neman hadin kansu don ganin jam’iyyar ta yi nasara a zabukan dake tafe.

A shekarar 2015 ne Alabde Abouba da wasu abokansa suka kafa jam’iyyar ta MPR bayan shafe shekaru 4 su na tafka shari’a akan maganar cancantar shugabancin jam’iyyar MNSD.

A yau jam’iyar na da kujeru 17 daga cikin 171 na wakilai a majalisar dokokin kasa.

Ga karin bayani a sauti:

Your browser doesn’t support HTML5

Jam'iyar MPR A Nijer Ta Ce Zata Tsaya Takara A Zabukan 2020 Da 2021