Zaben sabon sakatare jam’iya na kasa shine babban dalilin da ya sa uwar jam’iyar MNSD NASSARA kiran taron gaugawa bayan da aka kasa samun daidaito tsakanin wasu kusosinta na jihar Maradi wato sakatare mai barin gado ministan makarantun koyon aikin hannu Tidjani Abdoulkadri da mutunen da ya kamata ya canje shi Mahaman Doutshi. Bayan shafe awoyi ana tantauna mahalartan sun bayyana Me Mai Saley Djibrillou na reshen Zinder a matsayin sabon sakatare.
Shirye shiryen zabe donganin jam’iyar da dan takararta Seni Oumarou sun yi galaba a fafatawar 2020 da 2021 shine babban aikin da sabon magatakarda Me Mai Saley Djibrillou yace zai fi baiwa fifiko.
A jajibirin wannan taro an shafe wunin juma’a 14 ga watan Augusta da asabar 15 ga wata ana tafka shara’a bayan da sakatare mai baring ado Tidjani Abdoulkadri ya maka uwar jam’iya a kotu a bisa cewa bai gamsu ba da hanyoyin da aka bi wajen shirya zaben sabon sakatare mafari kenan alkalin kotun a matakin farko ya umurci uwar jam’iyar ta jingine wannan taro to sai dai kuma daga bisani kotun daukaka kara ta bada iznin a ci gaba da wannan zama.
Taron ya kaddamar wasu sabbin dokokin jam’iyar ta MNSD NASSARA da nufin saka tsari a sha’anin gudanar da ita sakamakon lura da yanayin da aka yi wannan zama. Kuma a cewar shugabanta bugo da Kari dan takara a zaben disambar 2020 Seini Oumarou dokokin jam’iya zasu daki duk wanda ya bijirewa ka’ida.
Kawo yanzu tsohon sakataren jam’iyar ta MNSD Tidjani Abdoulkadri wanda bai halarci wannan taro ba bai maida martani a game da zaben da ya dora Me Mai Saley Djibrillou akan wannan kujera ba.
Saurara karin bayani a sauti daga Souley Moumini Barma:
Your browser doesn’t support HTML5