Jam’iyar Awami League Ta Bangladesh Na Shirye Shiryen Yiwa Gwamnatin Rikon Kwaryar Kasar Bore

Yan Bangladesh a yayin wata zanga zanga a kasar

Mai yuwuwa ne nan bada jimawa ba yan Jam’iyar hambararriyar priministar Bangladesh Sheik Hasina su fita kan titi domin nuna kin jinin gwamnatin rikon kwaryar Muhammed Yunus, da ya taba samun kyautar nan mai daraja ta Nobel Peace prize, cewar jagoran jam’iyar.

Sakataren shirye shirye na jam’iyar Awami League Shafiul Alam Chowdhury, ya shaidawa muryar Amurka a ranar Juma’a cewa, sunanan suna shirye shiryen yin zanga zanga da fara fadi tashin su na siyasa.

Chowdhury na daga cikin gwamman shugabannin jam’iyar Awami League wanda ya arce daga Bangladesh, bayan da wani boren dandazon dalibai yayi waje da mulkin Hasina a watan Agusta. Shugabar, mace mai kamar maza na kan zagaye na hudu a shugabancin kasar ne a lokacin da daliban suka wartake ta, suka tilasta mata yin murabus a ranar 5 ga watan Agusta, inda ta arce zuwa Indiya cikin wani jirgin soji mai saukar angulu.

Tun bayan faduwar gwamnatin, an kama gwamman shugabanin jam’iyoyi da dama bisa alaka da yin diran mikiya kan masu bore, da yayi sanadiyyar mutuwar daruruwan mutane a sassan kasar tsakanin watan Yuli da Agusta. Dubban ma’aikatan Awami da magoya baya sun nemi mafaka a boye ta kasa, sakamakon tsoron kai musu hari.

A ranar Laraba ne, gwamnatin rikon kwaryar ta soke reshen daliban na jam’iyar Awami league na Bangladesh, inda ta Aiyana ta a matsayin kungiyar yan ta’adda.

A farkon watan nan kotun shari’ar laifuffuka ta kasar Bangladesh ta fitar da sammacin kamo tsohuwar priminista Hasina, da wasu su 45 dake da alaka da hambararriyar gwamnatin.

Da yake zantawa da muryar Amurka ta wayar tarho, Chowdhury yace, jam’iyar na aikin hada hancin yan jam’iyar tare da tuntubar sauran masu alaka da mukarraban siyasa domin kaddamar da yiwa gwamnatin rikon kwaryar bore.

A lokacin da aka tambaye shi, ko zuwa wane lokaci ne jam’iyar ke shirin fita kan tituna, jagoran na jam’iyar Awami League yace, bayan makonni biyu ne ko wata guda, za su bazama.

Manyan jam’iyun siyasa a Bangladesh sun marawa gwamnatin rikon kwaryar baya a burin ta na kawo sauye sauye a kasar, da suka ce jam’iyar Awami League ta wargaza da gagarumin tsoma bakin siyasa a cikin shekaru 15 din da suka wuce.

To sai dai duk da haka jam’iyun siyasa na nuna matsin lamba ga gwamnatin Yunus a fili, na ganin ta tabbatar da gaggauta dawowa kan turbar democradiyya. Daya daga cikin manyan jam’iyun siyasar kasar ba ta gamsu da irin tafiyar da akeyi ba ya zuwa yanzu.