Jakadiya Linda ta bukaci Rasha da ta dakatar da yakin tsakaninta da Ukraine, ta kuma fara bayar da gudummawar samar da abinci a duniya.
Jakada Greenfield ta bayyana haka ne a lokacin da ta kai ziyara a Arewa maso gabashin kasar Ghana, a wani bangare na ziyarar rangadin da ta ke yi a kasashen Ghana da Uganda.
Ziyarar Thomas-Greenfield dai ta kasance don tattaunawa kan yadda rikici tsakanin Rasaha da Ukraine ya kawo matsalar abinci a duniya. Da kuma ganawa da wasu manoma domin sauraron kalubalen da suke fuskanta.
Samun jari babbar matsala ce a fadar ta, don haka ne hukumar ta USAID ta sanar da bayar da kudade masu yawa don tallafa wa manoma, ta hanyar taimaka musu wajen magance kalubalen da su ke fuskanta. Dole ne mu shawo kan rikicin, kuma hanya daya tilo da za a iya shawo kan matasalar ita ce hada kai da aiki tare, a fadar ta.
A cewar Thomas-Greenfield, Ghana na da albarkatun da take bukata domin inganta samar da abinci.
Ta kuma tattauna da mata yan kasuwa da manoma domin sauraron kalubalen da suke fuskanta. Inda suka bayyana irin horo da suka samu wajen samun sabbin dabaru domin bunkasa harkokinsu.
Jakada Thomas-Greenfield ta ce gwamnatin Amurka ta na taimakawa manoma da dala miliyan 2.5 ta hanyar USAID a duniya.
Domin Karin bayani saurari rahotan Hawa AbdulKarim.
Your browser doesn’t support HTML5