Jakadiyar Amurka a Majalisar Dinkin Duniya, MDD Hikki Haley ta fadi jiya Talata cewa kasar Isira’ila ta yi taka tsantsan yayin da ta ke mai da martani a mummunan dauki ba dadin da ta yi da Falasdinawa a kan iyakar Gaza, sannan ta zargi kungiyar gwagwarmaya ta Hamas mai mulkin Gaza da tayar da fitinar.
Haley ta yi watsi da alakanta tashin hankalin da ake yi da bude Ofishin Jakadancinta da Amurka ta yi a Birnin Kudus ranar Litini.
Shi kuwa babban jami’in MDD Na Musamman Kan Tattaunawar Zaman Lafiya A Gabas Ta Tsakiya Nickolay Mladenov, yayin da ya ke magana da mambobin kwamitin daga Birnin Kudus, ya ce babu dalilin kashe-kashen.
“Shin wa zai iya bullo da kalamin da zai iya sanyaya zuciyar matar da aka kashe ma da? Wa zai iya?”
Jakadan kasar Kuwait a MDD Mansur al-Otaibi ya ce kasarsa “da kakkausan lafazi, ta na mai yin tir da kasshe-kashen da kasar Isira’ila ta yi jiya”
Taron gaggawan da Kwamitin Sulhun MDD ya kira jiya Talata, ya biyo bayan ranar da aka yi kashe-kashe mafi muni a Gaza a rigimar Isira’la da Falasdinawa cikin shekaru biyar da su ka gabata.
Gabanin taron na MDD, da yawa daga cikin kawayen Amurka da kuma masu adawa da ita, sun caccaki Amurka saboda bude Ofishin Jakadancin da ta yi a Birnin Kudus, da cewa hakan na iya tayar da hankali a Gabas Ta Tsakiya.
Mai magana da yawun Firaministar Burtaniya Theresa May y ace, “Ba mu amince da shawarar da Amurka ta yanke ta mai da Ofishin Jakadancinta zuwa Birnin Kudus tare kuma da amincewa da Birnin Kudus a Matsayin Babban Birnin Kasar Isira’ila ba”
Shugaban Kasar Faransa Emmanuel Macron ya yi tir da tashin hankalin da aka yi ranar Litini a Gaza. Shi ma Ministan Harkokin Wajen Rasha Sergey Lavrov ya yi ta jaddada adawar Rasha da matakin da Amurka ta dauka.
Shugabannin kasashen Larabawa ma sun yi Allah wadai da matakin na Amurka, ta yadda Firaministan Lebanon Saad Hariri ya kira matakin “takala,” shi kuma Ministan Harkokin Wajen Iran Mohammad Javad Zarif ya bayyana shi da “Ranar wani babban abin assha.”
Kasar Saudiyya kuma cewa ta yi ta na mai “yin tir da kakkausan harshe” da harbe Falasdinawa da Isira’ila ta yi a Gaza sannan ita ba ta amince da bude ofishin Jakadanci da Amurka ta yi a Birnin Kudus ba.
Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya fadi yayin wata ziyara a birnin London cewa canza ma ofishin jakadancin wuri “abin takaici ne”
“Kasancewa Amurka, wadda ke ikirarin zama mai shiga tsakani wajen tabbatar da zaman lafiya a yankin Gabas Ta Tsakiya da ma duniya baki daya, na da hannun a wannan kashe-kashen, ba abin yadda ba ne.”