Jakadiyar Amurka a Majalisar Dinkin Duniya, MDD,Niki Haley,jiya Lahadi ta gargadi shugaban Syria Bashar al-Assad cewa Amurka za ta sake kaiwa gwamnatinsa hari da makamai masu linzami, muddin ya sake amfani da makamai masu guba wajen kai wa mutanen kasar hari.
Madam Haley, ta gayawa tashar talabijin ta FOX cewa, idan har duk da makamai masu linzami 105 da Amurka da Britaniya da Faransa suka chulla kan mansana’antun sarrafa makaman masu guba a Syria ranar Asabar bai sa ya shiga taitayinsa ba, to ya shirya radadin sabbin hare hare masu zuwa, domin inji Haley, ba zamu kyale wani hari da makaman guba komin kankancinsa.
A halinda ake ciki kuma, fadar shugaban Amurka ta White House, ta ce har yanzu Amurka tana kan bakarta na janye sojojin Amurka daga Syria. Wannan furuci ya biyo bayan maganar da, shugaban Faransa Emmanuel Macron, ya yi cewa, ya shawo kan shugaban Amurka Donald, ya sake tunani kan shirin janye sojojin Amurka daga Syria, kuma ya takaita haren-haren da suka kai da makamai masu linzami.
shugaba Macron ya bayyana haka ne a hira da ya yi da tashar talabijin ta Faransa da ake kira BFM a jiya Lahadi, da cikarsa shekara daya akan mulki, kuma kwanaki biyu bayan da Faransa ta shiga jerin Amurka da Birtaniya wajen kai hari kan masana'antun harhada makaman guba na Syria.
"Kwanaki 10 da suka wuce shugaba Trump yana cewa tilas Amurka ta janye daga Syria, mun shawo kansa cewa tilas ne Amurka ta ci gaba da kasancewa a can na wani lokaci mai tsawo."