Na kasance mace ta farko da ta fara shirin siyasa a gidan radiyon da nake aiki duk kuwa da kallon gazawa da ake yi wa mata inji malama Khadija Aliyu.
Khadija ta ce ta nemi gurbin karatu na aikin likitanci ko zama malamar jinya amma hakarta bata cimma ruwa ba, domin bayan ta rubuta jarabawar shiga jami’a wato Jamb, bata sami nasara ba, amma ta sake gwadawa inda daga bisani ta sauya sheka inda ta sami gurbin karatu na aikin jarida.
Ta ce bayan samun aikin jarida ta zama mace ta farko da ta fara shirin ‘yan siyasa a inda ta sami aiki, duk kuwa da abokan aiki da dama na ikrarin cewar ba zata iya rike shirin ba.
Khadija ta ce kafin ta fara fuskantar kalubale a harkar aiki a jami’a ma ta fuskanci wasu kalubalen mussamam ma kasancewar ta cikin makaranta ne ta yi aure har ta haihu kafinta kammala karatunta na jami’a.
Khadija ta ce ko da kuwa ba abinda ran mutu ke so ba jajircewa na taimakawa mutum wajen cimma burinsa da nunawa al’umma babu abinda mutum ba zai iya ba muddin ya sa a ransa zai iya.
Ta dai ja hankali matasa da su maida hankali wajen neman ilimi domin a cewarta rayuwa ta canza sai da neman ilimi.
Your browser doesn’t support HTML5