Malama Fa'iza dai yar arewa maso gabashin Nijeriya ce wacce ta karanci harshen 'Turanci a jami'ar Maiduguri, dake jihar Borno, bayan kammala karatun ta, ta samu damar yi wa kasa hidima a jihar Sokoto inda ta fara da gabatar da labarai amma a irin na sansanin masu yi wa kasa hidima
Bayan kammala yi wa kasa hidima ta samu aikin jarida a jihar Kaduna inda daga nan ne ta fara aikin jarida ta kuma maida hankali har ta kai ta ga fara fasssara duk kuwa da cewar ita ba Bahausa ba ce, ta ce ta fuskanci matsaloli da dama.
Ta kara da cewa maida hankali da jajircewa ya sa ta fara koyon fassara da fita hada rahotannin wanda yanzu haka ta sami nasarar samun aikin jarida a kasar Sin.
Daga cikin kalubalen da ta fuskanta shine zama ita kadai ta yi wa kanta ci da sha da sauran abubuwan rayuwa , abu ne da bata saba da shi ba musamman a bakuwar kasa..
Fa'iza ta ce a yanzu suna da manhajan da mutum zai rubuta abin da yake so ga Basine sai manhajar ta fassara da haka ne ta ke mu’amala da mutanen Sin ta bakin Fa'iza Mustapha.
Your browser doesn’t support HTML5