Jagoran 'Yan Adawar Venezuela Ya Yi Tayin Ahuwa Ma Sojojin Kasar

Shugaban "yan Adawar Kasar Venezuela Juan Guaido

Shugaban ‘yan adawar kasar Venezuela kuma wanda ya ayyana kansa a matsayin shugaban kasa na riko, Juan Guaido, ya yi tayin yin ahuwa ma sojojin da suka goyi bayan dimokradiyya, su ka kuma yi watsi da gwamnati mai ci ta Maduro.

A wani taron manema labarai jiya Lahadi, Guaido ya ce ma sojojin, “Mu na jiranku, sojojin Venezuela. Mu na jiranku da kuma alkawarin da ku ka yi na kare kundin tsarin mulkin mu."

'Yan bangaren adawa, wadanda wasunsu ke tayar da murya su na cewa, "Abokina soja, kai ne kadai ake jira" ... sun yi ta raba takardu ma sojoji da 'yan sandan da aka tura masu dauke da bayanan shirin yin ahuwar.

Wadansu daga cikin sojojin su na jefar da takardun ko kuma su yaga, amma da yawa daga cikin sojojin Venezuela sun ce su da iyalansu sun gaji da tsananin karanci abinci da kuma sauran kayan more rayuwa.

A halin yanzu, shugaba Nicolas Maduro ya nace a jiya lahadi cewa, sojojin kasar su na bayansa a lokacin da ya ke kallon sojojin su na motsa jiki, inda suke amfani da nakiyoyin da aka yi a Rasha wadanda ake cilla su da roka da kuma bindigogin harbo jirgin sama.