Idan ta tabbata cewa Shugaban kungiyar ta'addancin nan ta ISIS ya mutu, to la-shakka an shiga wani sabon babi a tarihin duniya - musamman ma game da gwagwarmaya da makami da masu tsauraran ra'ayoyi ke yi.
WASHINGTON D.C. —
Rahotanni na nuna da alamar Abubakar al-Baghdadi, shugaban kungiyar ta’addancin nan ta ISIS, ya mutu a wani samamen yinkurin damke shi da sojojin Amurka su ka kai jiya Asabar a mabuyarsa.
Al-Baghdadi, wanda dan asalin kasar Iraki ne, wanda kuma sunansa na ainihi shi ne Ibrahim Awad al-Badri, ya yi shelar kafa abin da ya yi ikirarin daula ce ta Islama a watan Yunin 2014 a birnin Mosul, inda ya ayyana kansa a matsayin Khalifa.
A watan jiya, an ce wai, jagoran na ISIS, wanda bai cika fita bainar jama’a ba, ya fitar da wani sabon faifan bidiyo, mai nuna shi al-Baghdadin na kiran magoya bayansa da mayakansa da su dada daukar matakan soji su kuma dada yada farfagandarsu.