Tsohon shugaban Afrika ta Kudu, Jacob Zuma, ya yanke shawarar daina ba da bahasi a gaban wani kwamitin bincike da ake yi a baina jama’a, wanda ke zargin shi da cin hanci a lokacin mulkinsa.
Lauyoyin da suke kare Zuma, sun fada a yau Juma’a cewa, tambayoyin da ake yi wa Zuma ba su kamata ba kuma babu adalci a cikinsu.
A wannan makon tsohon shugaban ya ba da bahasi a gaban wani kwamitin bincike da gwamnati ta kafa.
Shugaban alkalan da ke binciken, Raymond Zondo, ya ce, ba hurumin kwamintin ba ne ya ayyana cewa wani na da laifi a wannan zama, sai dai aikin kwamitin ne ya gudanar da bincike kan wasu zarge-zarge da ake yi.
Shi dai Zuma ya sha musanta cewa ya aikata ba daidai ba, inda ya kan ce, binciken da ake yi a kansa, bita-da-kullin siyasa ne da nufin a bata masa suna.