Iyaye Na Dakon Jin Makomar Daliban Da Aka Sace A Najeriya

Your browser doesn’t support HTML5

Ashiru Adamu Idrisa, mahaifin da aka kwashe mai yara uku: “Abin da na gani ya matukar ta da min hankali, saboda ina kallo aka kwashe min ‘ya’ya, wannan ba karamin abin bakin ciki ba ne, yara uku aka kwashe min, dukkansu mata, shekarar karamar cikinsu biyar.”
Ashiru Adamu Idrisa, mahaifin da aka kwashe mai yara uku:
“Abin da na gani ya matukar ta da min hankali, saboda ina kallo aka kwashe min ‘ya’ya, wannan ba karamin abin bakin ciki ba ne, yara uku aka kwashe min, dukkansu mata, shekarar karamar cikinsu biyar.”

Sanusi Mustapha, Malami a makarantar Islamiyyar ta Salihu Tanko:
“A lokacin da suka zo, sai wasu daga cikinsu suka hau kyauren kofar makarantar suka duro ciki, sai muka ga sun rufe kofar makarantar yayin da mu kuma muna cikin ofis, sai kawai suka fara harbe-harbe, suka kwashe daliban.”

Shugaban Makaranta, Idris Umar:
“Daga alkaluman da muka tattaro daga iyayen dalibai, yara 136 ‘yan bindigar suka kwashe.” ​