Lauyoyin da suka kware akan al’amuran bakin haure sun ce iyalai sun shiga cikin damuwa bayan da wani mai shari’a a babban kotun Texas ya dakatar da wani shirin da gwamnatin Biden ta samar wanda zai baiwa iyalan Amurkawa damar zama ‘yan kasa.
Umarnin kotun da aka fitar a daren ranar Litinin ya biyo bayan da jihohi 16 suka kaliubalanci shirin wanda wani babban lauya dan Republican ya jagoranta.
Bakin haure akalla dubu 500,000 ne a kasar zasu amfana da shirin sannan da kuma akalla ‘yayansu su dubu 50,000.
Za a dakatar da shirin na tsawon kwanaki 14 sai dai kuma akwai yiwuwar a kara wa’adin dakatarwar. Hukumar kula da al’amuran bakin Haure ta ce gwamnati zata ci gaba da karbar takardun neman izinin zama ‘yan kasa yayin da take kokarin kare shirin a kotu.