An kafa ITF ne wajen shekaru arba'in da suka gabata yayinda turawan mulkin mallaka ke ficewa daga kasar domin a masu ma'aikatan da zasu maye guraben da suka bari..
Babban daraktan gidauniyar Sir Joseph Ari yace tunda shugaban Najeriya Muhammad Buhari ya ayana abubuwa biyar da gwamnatinsa zata mai da hankali a kai ya ga yakamata su ma a ITF su hada karfi da karfe wajen inganta horas da matasa sana'o'i daban daban.
Inji daraktan a Najeriya ne mutun zai yi karatu mai zurfi amma bai iya aikin hannu ba lamarin da ke hana kasar cigaba.
A wani sabon shirin da suka kirkiro hukumar zata bukace gwamnonin kasar 36 kowannensu ya basu matasan da zasu horas. Yace bayan matasan sun samu horo ba za'a barsu kara zube ba. Gidauniyar zta hada hannu da bankin masana'antu ya taimkawa matasan da jari.
Tun daga lokacin da aka kafa gidauniyar kawo yanzu ta horas da mutane fiye da miliyan goma.
Ga rahoton Zainab Babaji da karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5