Issoufou Mahamadou Ya Lashe Zaben Jamhuriyar Nijar

Shugaban Kasa Issoufou Mahamadou Na Jawabi Bayan Samun Nasarar Zabe

Hukumar zaben kasar Nijar ta bayyana shugaba Issoufou Mahamadou, a matsayin wanda ya lashe zaben da aka gudanar a ranar Lahadin da ta gabata, bayan da ya fafata da dan takarar ‘yan adawa Hama Amadou.

Ta hanyar wani kwarya kwaryan biki ne da aka gudanar tare da masu saka ido na kasa da kasa, shugaban hukumar zaben Nijar mai Shara’a Buba Ibrahim ya bayyana sakamakon zaben.

Shugaban hukumar zaben na cewa kashi 59.79 cikin 100 wanda aka kiyasta akan mutane Miliyan hudu da rabi suka kada kuri’a a fafatawar da Issoufou Mahamadou da Hama Amadou, kuma ya kara da cewa shugaban mai ci shine ya lashe zabe da kashi 92.49 daga cikin 100. Yayin da Hama Amadou ya sami kashi 7.51 daga cikin 100.

Tuni dai shugaba Issoufou Mahamadou ya kira taron manema labarai domin nuna farin ciki kan wannan nasara da ya samu.

Your browser doesn’t support HTML5

Issoufou Mahamadou Ya Lashe Zaben Jamhuriyar Nijar - 2'51"