Isra'ila Za Ta Fara Tsagaita Wuta A Kudancin Gaza

Dakarun Isra'ila (Hoto: AP)

A jiya Lahadi Isra'ila ta fadi cewa, zata fara tsagaita wuta a hare haren da take kai kan mayakan Hamas a kudancin Gaza tsawon sa’o’i 11 a duk rana, don bada damar kai karin kayan agaji ga Falasdinawan da ke fama da yunwa.

Gwamnatin kasar ta ce, dakatar da kai hare-hare a kudancin Gaza zai ci gaba da aiki har zuwa wani dan lokaci nan gaba, don ba manyan motocin agaji damar isa mashigar Kerem Shalom da ke karkashin ikon Isra'ila, wato babbar hanyar shigar da kayan agaji.

Kananan yara suna layi su karbi abinci a sansanin 'yan gudun hijira da keJabalia

Daga nan manyan motocin za su bi ta wata babbar hanya da ke kusa don kai kayan abinci da magunguna zuwa wasu sassan Gaza.

Tsagaita wuta da kai hare-haren da sojoji suka sanar, zai yi aiki ne a tazarar kilomita 12 a kan hanya a yankin Rafah amma ba zai yi aiki a Gaza ba, inda kasashen duniya ciki har da Amurka babbar abokiyar kawancen Isra’ila ke kokarin ganin Isra'ilar da Hamas sun cimma tsagaita wuta.

Palasdinawa su na Sallah Idi a Khan Yunis da ke kudancin Gaza

Kudurin tsagaita wutar da ake shirin yi zai dakatar da fada a duk fadin Gaza tsawon makonni 6, ya kuma bukaci a sako karin mutanen da Hamas ta yi garkuwa da su, da za a musaya da Falasdinawan da Isra'ila ke tsare da su.