Yayin da babban taron na Majalisar DinkinDuniya ke gudana, Isra’ila ta kara yin lugudan wuta a kan mayakan kungiyar Hezbullah da ta take ta auna su a kasar Lebanon ranar Talata, inda adadin wadanda suka mutu a hare-haren ta sama tun daga ranar Litinin da ta wuce ya karu zuwa 564, yayin da wasu 1,835 suka jikkata.
A jimullance, Isra’ila ta ce ta kai hari a wurare 1,600, inda jami’an kiwon lafiya na Lebanon suka ce an kashe yara 50 a wurare daban daban, tare da mata akalla 94.
Rundunar sojin Isra’ila ta ce hare-haren da ta kai a ranar Talata ya shafi wurare da dama da ta auna na kungiyar Hezbullah, ciki har da mayakan da ke da hannu wajen harba rokoki da dama a arewacin Isira’ila.
Isra’ila ta ce daya daga cikin hare-haren da ta kai a yankunan kudancin birnin Beirut ya kashe Ibrahim Muhammad Kobeisi, wanda Isra’ila ta bayyana a matsayin babban kwandan sojojin Hezbollah da ke sa ido kan tsarin makamai masu linzami na kungiyar.