Isra'ila Ta Haramtawa Ilham Omar da Rashida Tlaib Shiga Kasar Ta

Trump da Netanyahu

Kasar Isira’ila ta haramta shiga ma wasu ‘yan majalisar dokokin tarayyar Amurka biyu jiya Alhamis, wanda wannan zai tayar da wata sabuwar takaddama a muhawarar da ake yi, game da irin goyon bayan da Amurka ke bai wa wannan muhimmiyar kawar ta a yankin Gabas Ta Tsakiya.

‘Yan majalisar dokokin tarayyar Amurka Ilham Omar da Rashida Tlaib, sun sha caccakar kasar Isira’ila da manufofinta kan Falasdinawa. Da sun shirya kai ziyara Isira’ila da wasu birane da dama a Yamma da kogin Jordan cikin ‘yan kwanaki masu zuwa.

Mataimakiyar Ministan Harkokin Wajen Isira’ila Tzipi Hotovely, ta gaya ma wani dan jarida cewa, “Ba za mu kyale wadanda ba su kaunar ‘yancinmu na kasancewa cikin wannan duniyar su shigo cikin Isira’ila ba. Bisa ka’ida, daukar wannan mataki da mu ka yi, ya dace.”

Daf da bayar da sanarwar hanin, Shugaban Amurka Donald trump ya aike da sakon Tweeter da cewa, “Muddun Isira’ila ta amince ‘yan majalisa Omar da Tlaib su kai ziyara, hakan zai zama wata babbar gazawa. Sun tsani Isira’ila da dukkannin Yahudawa, kuma babu wani abin da za a fada ko a yi da zai canza masu ra’ayi.”