Isra’ila Ta Haramta Wa Guterres Shiga Kasar

  • VOA Hausa

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Guterres

A yau Laraba, Isra’ila ta ayyana cewa Sakatare Janar Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Guterres, ba nagartaccen mutum bane, inda ta zarge shi da gaza fitowa karara ya yi allawadai da harin makami mai linzamin da Iran ta kai mata.

“Duk mutumin da ya gaza fitowa karara yayi allawadai da mummunan harin Iran akan Isra’ila bai cancanci ya taka kafa zuwa kasarmu ba,” a cewar sanarwar da Ministan Harkokin Wajen Isra’ila, Isreal Katz, ya fitar.

“Wannan babban sakatare ne makiyin Isra’ila dake marawa ‘yan ta’adda da masu fyade da ‘yan ina da kisa baya,” a cewarsa.

A martaninsa ga harin makami mai linzamin da Iran ta kaiwa Isra’ila a daren jiya talata, Guterres yayi allawadai da kara fadadar rikici a yankin gabas ta tsakiya, inda ya koka akan yadda rikicin ke “kara kazancewa” a yankin.

“Wajibi ne a kawo karshen wannan. Gabadaya muna bukatar tsagaita wuta,” a cewar Guterres.

A jiya Talata Iran ta harba makami mai linzami kan Isra’ila, abinda ya sabbaba tashin jiniyar ankarar da kawo hari a birnin Tel Aviv da fadin Isra’ila a cewar ma’aikatar tsaron kasar.

Your browser doesn’t support HTML5

Iran Ta Harba Makami Mai Kinzami Kan Isra'ila

Wuta ta haskaka sararin samaniyar Isra'ila kamar yadda ma'aikatan kafar yada labarai ta NBC dake birnin tel aviv da yankin kan iyakar Lebanon na Tyre suka shaida sanda aka harba makami mai linzamin. An kuma hangi kananan tartsatsin wuta, wanda ake zaton sun taso ne daga kariyar kare makamai ta Isra'ila a yayin da kasar ke kokarin kare kanta daga harin.

An kuma jiyo karar wata fashewa a bidiyon da kafar yada labaran ta NBC ta nada, sai dai ba'a tantance ko karar ta haduwar makamai masu linzami a sararin samaniya ce ko kuma ta saukar makaman ce a cikin isra'ila.