A ranar Juma’a dakarun Isra’ila suka kaddamar da hare hare a yankin kudancin Beirut da yankunan dake kudancin Lebanon, da dakarun rundunar tsaron Isra’ila tace, sun gano cewa wuraren da Hezbollah keda karfi ne.
Wani faifan video da kafafen yada labarai suka samar sun nuna yadda aka kai hare hare a Baabda, Choueifat, Hadath da Dahiyeh dake kudancin Beirut.
Cikin wata wallafa ta kafar sadarwar zamani na X, dakarun rundunar tsaron Isra’ila tace, rundunar sojin saman ta sun kamala jerin hare hare kan hedikwatar da Hezbollah ke amfani da ita a yankin Dahiyeh a Beirut. Wallafar tace, an kai harin ne domin karya laggon Hezbollah na kaiwa Isra’ila hari, da ya hada da wuraren da suke kera makamai da kuma rumbunan makaman a Dahiyeh.
Hakazalika rundunar tsaron Isra’ila ka kara a shafin ta X cewa, a ranar Juma’a, kananan jiragen ta sun kaiwa Hezbollah hari a birnin Tyren na yankin kudanci, dake kusa da ruwa. Tace, wuraren da aka kaiwa hari sun hada da hedikwatar Hezbollah, kayayyakin leken asiri, rumbun ajiye makamai, da gine ginen soji.
Wallafar ta kara da cewa, da dama da ga kadarorin da aka kaiwa hari nada alaka da Hezbollah na Aziz, wanda daga nan ne ake harba makamai a yankin kudu maso gabashin Lebanon, da ya ratsa ta yankin kasar Isra’ila da sauran yankunan dake yankin.
A mabanbantar sanarwa, ofishin Majalisar Dinkin Duniya a Lebanon UNIFIL ya sanar cikin wata sanarwa a ranar Juma’a cewa, an raunata wasu ma’aikatan wanzar da zaman lafiya yan asalin Italiya a lokacin da aka harba rokoki biyu akan hedikwatar ofishin dake Shama, kusan kadan da kudancin Tyre. To said ai sanarwar tace, raunukan da suka samu ba masu barazana ba ne ga rayuwa, kuma ma’aikatan na samun kulawa a asibiti dake wurin.
Ofishin jami’an wanzar da zaman lafiyar na Majalisar Dinkin Duniya ya kara da cewa, rokokin sun lalata wani wurin boyewa hare hare da wuraren ajiye kayayyakin aiki, da jami’an tsaron kasa da kasa ke amfani da su, da haifar da mummunar barna ga gine gine dake kusa. Suka ce akwai yuwuwar Hezbollah ce ta kaddamar da harin, ko wasu kungiyoyi masu alaka da ita.
Sanarwar da ta fito daga ofishin tace, wannan harin shine na 3 akan hedikwatar ta da ke Shama a cikin mako guda, kuma an kai harin ne a tsakiyar lokacin tsananin barin wuta da hare hare ta kasa a yankunan Shama da Naqoura a yan kwanakin baya bayan nan, da ya kara haifar da zullumi a yankin.
Ofishin hukumar yayi furuci da kakkausar murya ga bangarorin masu fada da juna, da su kiyayi fada a kusa da inda cibiyar su take. Ta jaddada cewa, duk wani hari da aka kai kan jami’an wanzar da zaman lafiyar babban keta haddi ne ga dokokin duniya da yardadden kudurin kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya mail amba 1701.
Haka zalika, a ranar Juma’a ne ofishin Majalisar Dinkin Duniya mai kula da harkokin jin kai ya sanar cikin wata sanarwa cewa, shekarar bana itace mafi muni ga ma’aikatan jin kai a fadin duniya sakamakon rikicin da ake yi a Gaza.