‘Yan kungiyar ISIS sun kai wani harin makami mai guba a wani gari kusa da birnin Kirkuk dake Arewacin Iraki.
WASHINGTON DC —
Inda suka hallaka wata yarinya ‘yar shekaru 3 da haihuwa suka kuma raunata akalla mutane guda 600.
Wannan ne yasa daruruwan mutane kaura daga garin, kamar yadda jami’ai suka bayyana a jiya Asabar. Jami’an tsaro da ma’aikatan asibiti sun ce, harin farko da aka kai, an kai ne da sassafe a karamin garin Taza.
Firaministan Iraki ya tabbatarwa mutane cewa, wannan aika aikar ba zata tashi a tutar babu ba, dole sai hukuma ta hukunta masu alhakin kai harin.
Wani jami’i Adel Hussein yace, mata da yara na cikin fargaba a garin Taza, inda suke kira ga gwamnatin kasar da ta taimaka ta kai musu daukin gaggawa.
Adel yace masu binciken Jamus da Amurka sun isa garin don binciken gubar da aka harbawa garin.