Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Sandan Faransa Sun Cafke Masu Zanga-Zangar Kin 'Yan Gudun Hijira


Wasu 'Yan Sandan Faransa a Sansanin 'Yan Gudun Hijira Na Calais
Wasu 'Yan Sandan Faransa a Sansanin 'Yan Gudun Hijira Na Calais

‘Yan sandan Faransa sun kama mutane 14 bisa tuhumar yin zanga-zangar kin jinin zuwan ‘yan gudun hijira da ke sansanin Calais.

Inda masu zanga-zangar suka tare wata gadar motoci da kona tayoyi.Masu zanga-zangar da suka kira kansu da suna TAWAGAR SHAIDA ASALI.

Suna kira ne ga ‘yan gudun hijira da su bar musu garinsu su koma garuruwansu da suka fito. Inda suka rubuta a allunan da ke cewa BA HANYA - A KOMA GIDA.

Sun kuma fidda sanarwar da suka rabawa manema labarai tare da tare kan babbar gadar da bakin ‘yan gudun hijirar ke bi suna shigewa cikin kasar zuwa don isa Turai.

Calais da ta zama wani tarnakin ‘yan gudun hijirar da ke son shihga don isa cikin Birtaniya. Dubban mutane ne dai da ke gudun hijirar suka kafa katafaren sansanin da suke matsananciyar rayuwa a cikinsa.

Sannan akwai wasu kananan sansanonin da ke tsakanin arewacin tekun na Faransa.

XS
SM
MD
LG